Isa ga babban shafi
Belgrade

Kungiyar kasashe 'yan 'ba ruwanmu' ta cika shekaru 60

Wakilan kasashe da dama ne suka taru a  Belgrade, babban birnin kasar Serbia a yau, don bikin cika shekaru 60 na kungiyar kasashe ‘yan ba-ruwanmu, wato Non Aligned Movement.

Kasashe 120 'yan baruwanmu da masu sa ido  1na bikin cika shekaru 60 da kafuwar kungiyar.
Kasashe 120 'yan baruwanmu da masu sa ido 1na bikin cika shekaru 60 da kafuwar kungiyar. AP - Darko Vojinovic
Talla

A cewar ministan harkokin wajen Serbia, Nikola Selakovic, wakilan kasashe sama da 100, ciki har da ministocin harkokin waje 40 ne suke halartar taron, wanda ke gudana a karkashin tsauraran matakan kariya daga cutuka masu yaduwa.

Taron farko na wannan kungiyar da ta gudana a Belgrade a cikin watan Satumban shekarar 1961, ya samu halartar wakilan kasashe 25, ciki har da wadanda suka assasa ta kamar Firaministan India, Jawaharlal Nehru, shugaban Masar Gamal Abdel Nasser, shugaba Sukarno na Indonesia,  da Kwame Nkrumah na Ghana,  sai Josip Broz Tito na Yugoslavia. 

Selakovic ya ce taron bikin cika shekaru 60 da kafuwar kungiyar kasashe ‘yan ba ruwanmu ba shi da wani alkibla ta siyasa duba da cewa babu wata matsaya da za  a cimma, ko wata sanarwa da za a fitar, sai dai zai kasance wata hanya da kowa zai nuna ya tuna taron Belgrade na 1961 cikin shauki da alfahari.

Kungiyar ta kasashe ‘yan ba ruwanmu, wadda ta kunshi kasashe 120, da ‘yan kallo 17, ita ce hadaka mafi girma ta kasashe bayan majalisar dinkin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.