Isa ga babban shafi
Serbia-Kosovo

Serbia Taki Yarda Da Kosovo

Ministan Waje na kasar Serbia Vuk Jeremic, yau yayi gargadin cewa muddin kotun majalisar Dinkin Duniya ta zartas da baiwa kasar Kosovo ‘yancin kai, to kuwa akwai hatsari a cikinsa.Ministan na magana ne a Hague inda Kotun take, jin kadan kafin yanke shawara daga mashawarta na kotun kasa-da-kasa gameda ikirarin Kosovo na shekara ta 2008 na samawa kanta ‘yanci daga Serbia.Kamfanin Dillancin labarai na Serbia, Tanjug, ya jiyo daga bakin Ministan na cewa muddin aka baiwa Kosovo ‘yancin kai to kuwa akwai barazanar gaske ga makwabtan ta.Sai dai kuma yace shawaran da zaa tsayar, zasu duba sosai da idanun basira kafin bayyana mataki na gaba da zasu dauka.Ita dai kasar Serbia taki amincewa da ikirarin samun ‘yancin kai ko kuma warewa daga kasar Serbia da Kosovo tayi tun ranar 17 ga watan Janairu na 2008.  

Masu nuna kyamar  ware kasar Kosovo a Banja Luka
Masu nuna kyamar ware kasar Kosovo a Banja Luka rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.