Isa ga babban shafi
Afghanistan-G20

Shugabannin G20 za su ci gaba da aikin jin-kai a Afghanistan

Shugabannin Kungiyar kasashen G20 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya sun amince a tsakaninsu da su ci gaba da gudanar da aikin jin-kai a Afghanistan sakamakon matsalolin da suka addabi kasar.

Shugabannin kasashen G20 a yayin taronsu kan Afghanistan ta kafar intanet.
Shugabannin kasashen G20 a yayin taronsu kan Afghanistan ta kafar intanet. via REUTERS - PALAZZO CHIGI PRESS OFFICE
Talla

Shugaban Amurka Joe Biden da Recep Tayyip Erdogan na Turkiya da kuma Firaminsitan India Narendra Modi na daga cikin wadanda suka halarci taron ta bidiyo akan yadda za a tallafa wa kasar.

Firaministan Italiya Mario Draghi na daga cikin wadanda suke matsin lamba ga kungiyar wajen taimakawa kasar.

Shugaban China Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ba su samu damar halartar taron ba.

Tun bayan da Taliban ta karbe mulki a Afghanista, matsalolin kasar suka ta'azzara da suka hada da talauci, tabarbarewar tattalin arziki, take hakkin bil'adama da sauransu, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da babbar murya da a tallafa wa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.