Majalisar Dinkin Duniya ta tsawaita aikin ta a Haiti da watanni tara
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita aikin Majalisar a kasar Haiti da watanni tara bayan tattaunawar sa’o’i 11, ya haifar da da mai ido tsakanin mayan kasashen yamma da kuma China.
Wallafawa ranar:
Kwamitin ya gabatar da wani kuduri na tsawaita wa'adin da kasa da shekara guda kamar yadda Amurka ta nema, amma fiye da watanni shida da China ta bukata.
An kada kuri'ar amincewa da tsawaita wa’adin jim sa'o'i kadan kafin wa'adin aikin siyasa ya kare a kasar, inda aka tsawaita shi zuwa 15 ga watan Yulin shekarar 2022.
Yanzu haka kasar Haiti na cikin matsanancin rikicin siyasa, da tattalin arziki da kuma zamantakewa da tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu