Firaministan Haiti ya nada sabon ministan shari’a
Firaministan Haiti Ariel Henry ya nada sabon ministan shari’a kwana guda bayan ya kori mai gabatar da karar da ya bukaci yi masa tambayoyi saboda zargin da ake masa na hannu wajen kasha shugaban kasa Jovenil Moise.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwar da fadar shugaban kasar ta gabatar tace an nada Listz Quitel a matsayin ministan shari’a da kuma tsaron jama’a.
Kafin wannan nadi, Quitel na rike da mukamin ministan cikin gida tun daga ranar 20 ga watan Yuli.
Nadin ya zo ne yayin da rudani ya mamaye al'ummar Haiti, sama da watanni biyu bayan kisan da aka yi wa shugaban kasa a gidansa na sirri da tsakar dare, ta'addancin da tawagar miyagu dauke da makamai ta aiwatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu