Isa ga babban shafi
Haiti

Adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasar Haiti ya haura dubu 2

Hukumomin kasar Haiti sun ce adadin mutanen da girgizar kasar da aka samu makon jiya ta kashe ya karu zuwa dubu 2 da 207.

Ma'aikatan agaji yayin aikin rabon abinci a garin Les Cayes da girgizar kasa ta afkawa a kasar Haiti, August 20, 2021.
Ma'aikatan agaji yayin aikin rabon abinci a garin Les Cayes da girgizar kasa ta afkawa a kasar Haiti, August 20, 2021. Reginald LOUISSAINT JR AFP/File
Talla

Hukumar bada agajin gaggawar kasar ta ce an gano wasu sabbin gawarwaki a kudancin kasar, yayin da har yanzu ake neman mutane 344 da suka bata kuma har yanzu ba a ji duriyar su ba.

Gwamnatin Haiti ta ce akalla mutane dubu 600 girgizar kasar ta makon jiya ta shafa.

Wata sabuwar barazana kuma da ma’aikatan agaji ke fuskanta a ita ce harin da gungun mutane zauna gari banza ke kai musu, abinda ya haifar da cikas ga aikin raba kayan agaji ga wadanda suka tsira daga iftila’in girgizar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.