Isa ga babban shafi
Haiti - Girgizar kasa

Kayayyakin agaji sun fara isa yankunan da girgizar kasa ta shafa a Haiti

Ana sa ran jirgin ruwan sojin Faransa ya isa Haiti da tan 40 na kayayyakin agaji da ruwan sha, da kuma jirgi mai saukar ungulu don taimaka wa wadanda iftila’in girgizar kasa ya rutsa da su.

Kokarin rabon kayan abinci ga wadanda suka tsira daga girgizar kasar Haiti.
Kokarin rabon kayan abinci ga wadanda suka tsira daga girgizar kasar Haiti. Reginald LOUISSAINT JR AFP
Talla

Kayayyakin agaji daga kasashen duniya sun fara isa yankunan karkara a kudu maso yammacin Haiti tun daga ranar Alhamis, kwanaki 5 bayan da karkarfar girgizar kasa ya kashe sama da mutane 2100 ya kuma rusa dubun dubatan gine gine.

 Zaftarewar laka da aka samu sanadiyar mamakon ruwan sama da aka shafe kwanaki biyu ana a yi a farkon wannan makon ya tare wani bangare na hanyar  shiga yankin, kuma karin wani ruwan saman a iya datse hanyar kacokan.

Farashin kananan jakunan ruwan sha ya karu har ninki 3 tun bayan girgizar kasar, a cewar wasu wadanda suka tsallake rijiya da baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.