Karin kasashe sun dakatar da zirga-zirga tsakaninsu da Afirka ta Kudu
Amurka, da Canada da Australia sun shiga jerin kasashen da suka dakatar da zirga-zirga tsakaninsu da Afirka ta Kudu a ranar Asabar, bayan gano sabon nau’in cutar Korona na Omicron a kasar, wanda a yanzu haka ya firgita hukumomin kasa da kasa.
Wallafawa ranar:
Tuni dai gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayyana bacin ranta kan matakin rufe ‘yan kasar iyakoki da kasashe da dama suka yi.
Kawo yanzu tuni Biritaniya, Jamus da Italiya da kuma Jamhuriyar Czech suka tabbatar da bullar sabon nau’in cutar Koronar na Omicron a cikinsu.
A baya bayan nan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa sabon nau’in cutar na Korona na iya yaduwa cikin sauri fiye da sauran nau’ikan annobar.
A bangaren kwararru kuwa, sun yi gargadin cewa mai yiwuwa hukumomi sun lattin daukar matakin hana tafiye-tafiye don dakile yaduwar sabon nau’in Koronar na Omicron zuwa sassan duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu