Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Afirka ta Kudu ta caccaki kasashen da suka soke zirga-zirga da ita saboda Korona

Ma'aikatar lafiyar Afirka ta Kudu ta caccaki kasashen da suka haramta zirga-zirga tsakaninsu da kasar don dakile yaduwar sabon nau’in cutar Korona, matakin da Afirka ta Kudun ta bayyana a matsayin mugunta, da rashin kwarewa a fannin kimiyya, wanda kuma ya sabawa shawarar hukumar lafiya ta duniya WHO.

Mutane sun yi layi don hawa jirgin Air France zuwa Paris a filin jirgin sama na OR Tambo a birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu. 26 ga Nuwamba, 2021.
Mutane sun yi layi don hawa jirgin Air France zuwa Paris a filin jirgin sama na OR Tambo a birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu. 26 ga Nuwamba, 2021. © AP
Talla

Yanzu haka dai bayanai sun tabbatar da cewar, sabon nau'in Koronar mai suna Omicron da ya bulla daga Afirka ta Kudu, ya bazu zuwa Hong Kong, Belgium, Isra'ila da kuma Botswana.

Biritaniya ce dai kasa ta farko da ta dauki matakin haramta zirga-zirga tsakaninta da kasashen kudancin Afirka, sa'o'i kadan bayan da Afirka ta Kudu ta bayyana gano sabon nau’in Koronar na Omicron da ke iya rikidewa zuwa wasu karin sabbin nau’ikan.

Daga bisani ne kuma kasashen Austria, Canada, Faransa, da Jamus, da Italiya, da Netherlands da kuma Amurka suka bi sahun Birtaniyar wajen dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga yankin kudancin nahiyar Afirka, musamman ma daga Afirka ta Kudun.

Sai dai kuma a ranar Juma’a hukumar lafiya ta Duniya WHO ta yi kira ga kasashe da su guji daukar matakin na haramta zirga zirga da wata kasa ko yanki a wannan mataki da ake ciki.

A halin da ake ciki dai, cin-cirindon matafiya sun kasance tsaye kan dogayen layuka a filin jiragen sama na kasa da kasa dake birnin Johannesburg tun a ranar Juma’a da zummar hawa jiragen da za su yi balaguron karshen ficewa daga Afirka ta Kudu, biyo bayan matakin haramta zirga-zirgar da kasashe da dama suka dauka tsakaninsu da kasar, bayan gano sabon nau’in cutar Korona na Omicron.

Akasarin matafiyan dai sun yanke hutu ko kuma yawon bude idon da suke yi a Afirka ta Kudun ne, gudun kada haramcin tafiye-tafiye tsakanin baki daga kasar zuwa yankunansu ya rutsa da su na tsawon lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.