Isa ga babban shafi
Duniya-AIDS

Shekaru 40 bayan gano cutar AIDS masana sun gaza samar da maganinta

Yau Duniya ke bikin ranar yaki da cutar AIDS ko kuma Sida a wani yanayi cike da fatan lalubo maganin cutar bayan shafe shekaru 40 da gano ta amma ba tare da magani ko kuma rigakafinta ba, face kwayoyin rage tasirinta a jikin masu dauke da ita.

Dubban mutane ke mutuwa kowacce shekara sanadiyyar cutar ta HIV AIDS ko kuma Sida.
Dubban mutane ke mutuwa kowacce shekara sanadiyyar cutar ta HIV AIDS ko kuma Sida. REUTERS/Rupak De Chowdhuri
Talla

Yunkurin yakar cutar da Majalisar Dinkin Duniya ke yi karkashin shirin UNAIDS cike da fatar samar da maganin na AIDS kafin shekarar 2030 ya ci karo da babban kalubale bayan bullar cutar covid-19 da ta kawo tangarda a yaki da kusan dukkanin cutuka masu hadari.

Tun daga shekarar 1988 ne Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowacce ranar 1 ga watan Disamba don yaki da cutar da AIDS da kuma wayar da kai game da illarta bayan da ta shiga jerin cutuka mafiya hadari da kuma ke kisa ba kakkautawa.

A shekarar 1981 ne aka faro ganin yanayin cutar jikin wasu masu auren jinsi a California amma sai tsakiyar 1982 aka yi tantance cutar tare da bata suna, yayinda a shekarar 1983 aka gano kwayar cutar da ke haddasa AIDS din wato HIV.

Shekaru bayan gano kwayar cutar ne masana a Amurka makyankyasar cutar suka samar da magunguna rage kaifinta da aka yiwa lakabi da AZT a shekarar 1988 lokacin ana da mutum dubu 150 jumullar masu da AIDS a Duniya baki daya, kuma a wancan lokaci ne aka fara wayar da kai a kokarin yakarta la’akari da yadda ta ke fantsamuwa.

Daga shekarun 1990 ne aka fara samun mutuwa sanadiyyar cutar kuma mutum na farko da ta kashe shi ne jarumin Amurka Rock Hudson kana mawakiyar Birtaniya Freddie Marcury da kuma Rudolf Nureyev dan rawa daga Rasha.

A shekarun 1994 cutar ta AIDS ta zama mafi kisa ga matasan Amurka galibi wadanda shekarunsu ya fara daga 25 zuwa 44 gabanin 1996 da kasar ta yi nasarar samun raguwar masu dauke da cutar.

Daga shekarun 1999 ne jumullar masu dauke da cutar ya kai miliyan 50 a sassan Duniya yayinda ake samun karuwar mace mace bayan rasa rayukan mutane miliyan 16 la’akari da tsadar kwayoyin rage kaifinta da Amurka ta samar.

Alkaluman WHO na nuna cewa har yanzu nahiyar Afrika ke kan gaba a jerin yankunan da ke da yawan masu fama da wannan cuta ta HIV AIDS tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu.

Wani rahoton UNAIDS ya koka da yadda kashi 2 bisa 3 na masu dauke da cutar ke rayuwa ta hanyar dogaro da magungunan rage kaifin cutar.

Alkaluman UNAIDS ya nuna cewa cikin shekaru 40 bayan bullar cutar ta AIDS ko kuma sida ta hallaka mutane miliyan 36 da dubu 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.