Isa ga babban shafi
Vatican-Kirsimati

Fafaroma na son a cimma matsaya kan yaki da Omicron

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis ya bukaci zaman tattaunawa domin cimma matsaya game da batun killace masu fama da annobar Korona, a daidai lokacin da miliyoyin mabiya addinin Kirista ke bikin Kirismati a yau Asabar .

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis
Shugaban Darikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis REUTERS - YARA NARDI
Talla

Sabon nau’in cutar Korona da aka yi wa lakabi da Omicron ya rage armashin bikin na Kirismati a bana, inda ‘yan uwa da abokan arziki suka gaza samun damar walwala tare kamar yadda aka saba kafin bullar Korona.

Wasu gwamnatocin kasashen duniya musamman a Turai sun sake tsaurara dokokin yaki da cutar da zummar takaita yaduwar Omicron a yayin bikin na Kirismati, lamarin da bai yi wa wasu mutane dadi ba.

A bangare guda, Fafaroman wanda ya gabatar da jawabinsa ga mutanen da adadinsu bai wuce dubu 2 ba a fadar Vatican, ya koka kan yadda ake yin watsi da halin da al’ummar Yemen da Syria da Iraqi  ke ciki, yayin da kuma ya yi gargadi game da barkewar sabon rikici a Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.