Isa ga babban shafi
Sabuwar Shekara

Duniya na bikin sabuwar shekara cike da fargabar Omicron

Duniya ta shiga sabuwar shekarar 2022 cike da fargabar nau’in corona na Omicron da ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a sassa daban-daban, dai dai lokacin da kasashe da dama ke sabunta dokokin yaki da cutar a bangare guda kuma WHO na gargadin daukar makamantan matakan 2020 da ya kassara tattalin arzikin Duniya.

Bikin sabuwar shekara a birnin Floridan Amurka.
Bikin sabuwar shekara a birnin Floridan Amurka. AP - Rob O'Neal
Talla

Annobar ta corona wadda ta shiga shekara ta 3 da zama babbar barazanar Duniya ta kashe mutane fiye da miliyan 5 da dubu dari 4 tun bayan bullarta a yankin Wuhan na tsakiyar China cikin watan Disamban 2019.

Duk da cewa an shiga shekarar 2021 da ta gabata da farin cikin samar da alluran rigakafin cutar, a wannan karon an shiga sabuwar shekarar ta 2022 cike da hasashen yiwuwar kawo karshen cutar bayan hasashen masana daga hukumar lafiya ta Duniya.

Faransa ce kasar da sabon nau'in corona na Omicron ya fi tsananta bayan da a jiya juma'akasar ta samu kusan mutum dubu 230 sabbin harbuwa cikin kasa da sa'o'i 24, matakin da kuma ya hana gudanar da bikin sabuwar shekara kamar yadda aka saba.

Birnin New York na Amurka dai ya dawo da bikin sabuwar shekara kamar yadda ya saba gabanin zuwan corona sai dai bisa matakan sanya takunkumi da dakile yaduwar cutar haka zalika an kayyade yawan mutanen da za su halarci bukukuwan sabanin yadda aka saba cincirindo.

Wasu yankuna na Spain sun gudanar da bikin sabuwar shekarar tamkar babu corona duk da cewa dai kashi 50 na yawan mutanen da suka saba taruwa ne suka yi gangamin bisa matakan kariya, haka zalika birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa wanda mahukuntansa suka ware sassa har 29 da aka gudanar da bikin bisa tsauraran matakan hana yaduwar corona.

A Faransa bikin ya gudana da dan sassauci idan aka kwatanta da bara amma dai a wannan karon ma karkashin tsauraran matakan hana yaduwar cutar, duk da cewa an soke shagulgula da dama ciki har da gagarumin wasan wutar da aka saba gudanarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.