Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

An fara tattaunawa tsakanin wakilan Rasha da na Ukraine a iyakar Belarus

Wakilan kasashen Rasha da na Ukraine sun fara tattauna akan iyakar Belarus da nufin tsagaita wuta a yakin da ya barke tsakanin kasashen biyu makwabtan juna, tattaunawar da ke zuwa a dai dai lokacin da Sojin Kiev ke kora dakarun Moscow zuwa wajen birnin da suke kokarin yiwa mamaya.

Ministan tsaron Ukraine Oleksii Reznikov tare da tawagar da za ta jagoranci tattaunawa da wakilan Rasha a iyakar Belarus.
Ministan tsaron Ukraine Oleksii Reznikov tare da tawagar da za ta jagoranci tattaunawa da wakilan Rasha a iyakar Belarus. AFP - SERGEI KHOLODILIN
Talla

Ministan tsaron Ukraine Oleksii Reznikov ne ke jagorantar tawagar kasar a tattaunawar ta yau litinin, yayinda Vladimir Medinsky babban hadimin Vladimir Putin ke jagorantar tawagar Rasha.

Tuni dai dakarun Rasha suka kwace iko da gabashin birnin Kharkiv bayan da aka shiga rana ta 5 da fara farmaki kan sassan kasar ta Ukraine.

Wasu majiyoyin labarai sun ce har zuwa yanzu Rasha ba ta kama wani muhimmin birni ba tun bayan fara farmakin, yayinda ta sake jibge tarin dakarun akan iyaka tun da sanyin safiyar yau.

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya bayyana cewa Rasha ba za ta sanar da matsayarta ba, har sai an kammala tattaunawar ta yau.

A bangare guda fadar shugaban Ukraine dai ta bukaci tsagaita wuta cikin gaggawa tare da janye dakarun bangarorin biyu tun gabanin shiga tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.