Isa ga babban shafi
MDD-Rasha-Amurka

MDD da Amurka za su yi zama kan Rasha bayan umarnin Putin ga sashen nukiliya

A yau litinin za a gudanar da taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya domin tafka mahawara dangane da rikicin Rasha da Ukraine, yayin da a nasa bangare shugaba Joe Biden ke shirin zantawa da shugabannin kasashe kawayen Amurka bayan da shugaba Vladimir Putin ya sanar da cewar yanzu haka cibiyoyin makaman nukiliyar kasar na cikin shirin ko-ta-kwana.

Wani yanki da Sojojin Rasha suka tarwatsa a Ukraine.
Wani yanki da Sojojin Rasha suka tarwatsa a Ukraine. AFP - SERGEI SUPINSKY
Talla

A daidai lokacin da alkalumma ke nuni da cewa adadin fararen hula da suka rasa rayukansu a wannan rikici ya zarta 352 ne, shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayar da umurni ga cibiyoyin makaman nukiliyar kasar da su kasance a cikin shirin ko-ta-kwana, matakin da ya haifar da suka daga kasashen duniya.

A yau litinin za a gudanar da Taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya domin tafka mahawa dangane da halin da ake ciki, yayin da a hannun daya shugaba Joe Biden zai zanta ta wayar tarho da shugabannin kasashe kawayen Amurka domin daukar mataki na ba-daya a kana bin da suka kira mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

Sanarwar da fadar gwamnatinn Amurka ta fitar game da wannan tattaunawa na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da shugaban Majalisar gudanarwar Turai Joseph Borell ya sanar da cewa Turai za ta taimaka wa Ukraine da kayan aikin soji ciki kuwa har da jiragen yaki domin kare kanta daga Rasha.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Ukraine ta amince ta tura tawaga don fara tattaunawar sulhu da jami’an Rasha tare da shiga tsakanin shugaban Belerus Alexandre Lukachenko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.