Isa ga babban shafi
Rasha - Ukraine

'Yan sandan Rasha sun kama masu adawa da mamaye Ukraine fiye da dubu 3

Jami’an tsaron Rasha sun kama 'yan kasar fiye da dubu 3,000 saboda gudanar da zanga-zangar kin jinin yakin da gwamnatin shugaba Vladimir Putin ya kadamar kan Ukraine a ranar Alhamis ta makon jiya.

Jami’an ‘yan sanda yayin tsare wata mata a birnin St. Petersburg na kasar Rasha, Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022.
Jami’an ‘yan sanda yayin tsare wata mata a birnin St. Petersburg na kasar Rasha, Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022. © AP Photo/Dmitri Lovetsky
Talla

Kungiyar farar hula da ke sa ido kan lamurran da suke faruwa mai suna OVD-info, ta ce a kalla mutane dubu 3 da 52 ake tsare da su yanzu haka a Rasha, inda ta ce a ranar Asabar kadai mutane 467 aka kame a garuruwa 34.

A baya bayan nan hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasar Rasha ta haramtawa kafafen yada labarai masu zaman kansu kwatanta harin da Moscow ta kai kan Ukraine a matsayin “mamaya” ko kuma shelanta yaki".

Yayin da sojojin Rasha suka shiga birnin Kyiv na Ukraine, ma'aikatar tsaron Moscow ta umarci kafafen yada labaran Rasha su tsaya kan bayar da alkaluman da suka faru a hukumance.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa ta zargi wasu kafafen yada labarai masu zaman kansu da yada bayanan da ba su da tabbas a cikin al'umma game da hare-haren da sojojin Rasha suka yi a garuruwan Ukraine da kuma kashe fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.