Isa ga babban shafi

Jama'ar Sri Lanka sun fusata bayan da yan sanda suka bude wuta

Ministan tsaron kasar Sri Lanka ya bayar da umurnin bude wuta a kan masu tarzoma da ke wawashe ko barnata dukiyar jama’a, bayan da masu zanga-zanga suka fara afka wa gidajen ‘yan siyasa da kuma sauran manyan jami’an gwamnatin kasar.

Zanga-zanga a kasar Sri Lanka
Zanga-zanga a kasar Sri Lanka AP - Eranga Jayawardena
Talla

Yanzu haka dai an baza dubban jami’an tsaro a kan titunan birnin Colomba, don kawo karshen tarzomar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 8 da kuma raunata akalla 65 ciki har da jami’an tsaro, yayin da aka ruwaito cewa an kona motoci kusan 90.

Firaministan kasar ya sauka 

Firaministan Sri Lanka Mahinda Rajapaksa ya sauka daga mukamin sa sakamakon zanga zangar adawa da gwamnati da ta rikide ta zama tashin hankali, abinda yayi sanadiyar mutuwar mutane 5 cikin su harda Dan Majalisar dokoki, yayin da wasu mutane kusan 200 suka samu raunuka.

Firaministan Sri Lanka, Mahinda Rajapaksa, wanda ya yi murabus.
Firaministan Sri Lanka, Mahinda Rajapaksa, wanda ya yi murabus. © AFP

Rahotanni sun ce wani dan majalisa Amarakeerthi Athukorala daga Jam’iyya mai mulki ya harbe wasu mutane 2, ciki harda wani matashi mai shekaru 27 da yam utu, kafin daga bisani shima ya kasha kan sa lokacin da masu zanga zangar suka masa kawanya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.