Isa ga babban shafi

Macron na son a bai wa Afrika babban matsayi a G20

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana goyon bayansa kan bai wa tarayyar Afrika kujerar din-din-din a kungiyar G20 ta mafiya karfin tattalin arzikin duniya, kwatankwacin wadda tarayyar Turai ke da ita.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron © AFP - LUDOVIC MARIN/POOL
Talla

A jawabinsa gaban manema labarai a tsibirin Bali, shugaba Macron ya ce kamar yadda kungiyar Tarayyar Turai EU ke da ta cewa, a cikin G20 kamata ya yi ita ma AU ta samu makamancin matsayin.

Zuwa yanzu dai Afrika ta kudu ce kasa daya tilo daga nahiyar Afrika da ke cikin kungiyar ta G20, guda cikin manyan kungiyoyi da ke cimma matsaya game da muhimman batutuwan duniya.

Shugaba Macky Sall na Senegal da ke jagorancin kungiyar tarayyar Afrika, ya bukaci samun wakilcin kassahen Afrika a manyan hukumomin da suka kunshi kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da kuma G20.

Sall da shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta Kudu da ke halartar taron na G20 a tsibirin Bali na Indonesia ko cikin watan Oktoba sun nanata bukatar cewa wajibi ne manyan kasashen duniya su girmama muradan kowanne sashe ko kuma fuskanci hadarin yankan kauna.

Macron a jawabin da ya gabatar, ya bayyana shirin kiran wani taron kasa da kasa kan sabuwar huldar kasuwancin Faransa da Afrika ta kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.