Isa ga babban shafi

RSF ta sanar da kisan 'yan jaridu dubu 1 da 700 cikin shekaru 20

Kungiyar ‘yan jaridun kasa da kasa ta Reporters Without Borders ta sanar da kisan ‘yan jarida akalla dubu 1 da 700 cikin shekaru 20 da suka gabata alkaluman da ke nuna kisan akalla ‘yan jarida 80 ko fiye a kowacce shekara.

Kasashen Syria da Iraqi ne kan gaba a sahun kasashen da aka fi kisan 'yan jaridu cikin shekaru 20 da suka gabata.
Kasashen Syria da Iraqi ne kan gaba a sahun kasashen da aka fi kisan 'yan jaridu cikin shekaru 20 da suka gabata. AFP - PHILIPPE LOPEZ
Talla

Kungiyar wadda ke da shalkwata a birnin Paris, ta ce daga shekarar 2003 zuwa 2022 a lokacin ne ‘yan jaridu suka fuskanci mafi munin tashin hankali ta yadda aka rika kashe su ba kakkautawa a kokarin dakile aikinsu na ‘yancin bayar da bayanai.

Kungiyar ta Reporters Without Borders ta ce a kowacce shekara ana samun kisan ‘yan jarida fiye da 80 a tsakanin shekarun na 2022 zuwa bana, wanda ke nuna yadda rayuwar masu wannan aiki ta kai kololuwar hadari duk da ikirarin aiwatar da dokar ‘yancin fadar albarkacin baki.

Sakatare janar ta RSF Christope Deloire ta ce karkashin wannan adadi akwai tarin fuskoki da ayyukan mutanen da suka sadaukar da rayukansu a kokarin wadata jama’a da bayanai.

Kasashen Syria da Iraqi s uke matsayin mafiya hadari ga ‘yan jarida inda aka kashen ‘yan jaridun 578 cikin shekarun 20 a kasashen biyu wanda ke matsayin fiye da rabi na adadin ‘yan jaridun da aka kashe a duniya baki daya a shekarun.

Sauran kasashen da suka yi kaurin suna wajen kisan ‘yan jaridan sun kunshi Mexico da mutum 125 kana Philippines me ‘yan jarida 107 Pakistan 93 Somalia 78.

RSF ta bayyana cewa tsakanin shekarar 2012 zuwa 2013 kadai sai da aka kashe ‘yan jarida 144 yayinda aka kara kashe wasu 142 a shekarar da tta biyo baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.