Isa ga babban shafi

An aikata abin kunya a Congo - Fafaroma

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis da ke ziyara a nahiyar Afrika, ya caccaki abin da ya kira “ manyan laifuka” da suka janyo wa daukacin  bil’adama  kunya a yankin gabashin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo.

Fafaroma Francis tare da dandazon jama'a a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Demokuradiyar Congo
Fafaroma Francis tare da dandazon jama'a a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Demokuradiyar Congo REUTERS - YARA NARDI
Talla

Fafaroma Francis ya bayyana haka a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Demokuradiyar Congo bayan ya kammala sauraren koken mutanen da aka ci zarafinsu a  rikicin kasar, yayin da ya  yi kira ga tsageru da su ajiye makamansu.

A yayin gabatar da jawabinsa a gaban dandazon jama’a fiye da miliyan guda, Fafaroman ya yi wa ‘yan kasar kashedi, yana mai cewa, kuna azurta kanku ta haramtacciyar hanya gami da salwantar da  rayukan mutanen da ba su-ji-ba-su-gani-ba.

‘Ku saurari kukan da jininsu ke yi’ inji Fafaroman wanda ya yi ishsra zuwa ga wata aya a littafin Genesis, yayin da ya roki rahamar Allah don gyara zukatan bata-gari na kasar.

Tun a karshen 2021 ne, ‘yan tawayen M23 suka karbe yankuna da dama a lardin Arewacin Kivu a can gabashin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo, lamarin da ya tilasta wa dubun-dubatan jama’a kaurace wa muhallansu, baya ga wadanda suka rasa rayukansu.

Kazalika yankin ya yi fama da hare-haren mayakan ADF masu ikirarin jihadi, wadanda a kwanakin baya suka kai harin da ya kashe mutane 14 a wata majami’a.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.