Isa ga babban shafi

An samu mummunan koma baya a kare hakkin mata cikin 2022- Rahoto

Dai dai lokacin da ake shirin gudanar da bikin ranar mata ta Duniya a ranar 8 ga watan Maris, wasu alkaluman sun nuna yadda aka mummunan koma baya a kare hakkin mata a kasashe daban-daban ciki har da raguwar ‘yancin karatu da dakile ‘yancin zubar da ciki da hana su madafun iko a wasu sassa.

Matan Afghanistan su ne kan gaba wajen fuskantar take hakki bayan matakin gwamnatin Taliban na hanasu karatu da aiki.
Matan Afghanistan su ne kan gaba wajen fuskantar take hakki bayan matakin gwamnatin Taliban na hanasu karatu da aiki. AFP - -
Talla

Alkaluman da kungiyoyin mata suka tattara sun nuna yadda aka samu koma baya a kare hakkin matan a kusan dukkanin sassan duniya kama daga Turai zuwa yankin Asiya da kuma Afrika, ta fuskar ‘yancin karatu ko kuma tofa albarkacin bakinsu.

Alkaluman sun fara da yadda ake samun take hakkin matan da ke neman ‘yancin zubar da ciki a Amurka da kasashen Turai, inda zuwa yanzu jihohi akalla 20 cikin 50 suka doge kan dokar 1973 da ta haramta zubar da ciki a kasar mai rajin tabbatar da ‘yancin mata

Gamayyar kungiyoyin matan ta koka da koma bayan, duk da tsaurara kiraye-kirayen ta na ganin matan sun nuna kafiya wajen tabbatar da ‘yancinsu.

Baya ga jihohin Amurka da ke tirjiya kan dokar zubar da cikin wasu sassa na Turai sun ki amincewa da bai wa matan ‘yancin zubar da ciki inbanda a kasashen Hungary da Spain yayinda har yanzu likitoci ke kin amincewa da zubarr da jiki a kasashen Hungary da Poland.

Can a Iran kuwa da sauran kasashen yanking abas ta tsakiya kungiyoyin sun koka da yadda Mata kef ama da rashin ‘yanci kan suturar da suke sawa, bayan kisan Mahsa Amin ikan rashin saka hijabi da ya haddasa kakkarfar zanga-zanga a sassan Tehran cikin 2022.

Kungiyoyin sun kuma kafa hujja da yadda Mata a Afghanistan ke fama da rashin ‘yancin karatu da aiki karkashin gwamnatin Taliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.