Isa ga babban shafi

Yau duniya ke bikin ranar mata cike da fargabar karuwar cin zarafi

Yau duniya ke bikin ranar mata kamar yadda aka saba kowacce shekara, ranar da ke da nufin jaddada manufar samar da daidaito tsakanin jinsin na Mata da takwarorinsu Maza, bikin da a wannan karon ke zuwa cike da fargabar karuwar take hakkin Matan a sassa daban-daban kama daga Turai da Amurka da kuma Afghanistan.

Matan yankin Diyarbakir na kasar Tukiya  na bukin ranar mata cikin shigen al'adun su na gargajiya a ranar 8 ga watan ,Maris na shekarar 2021
Matan yankin Diyarbakir na kasar Tukiya na bukin ranar mata cikin shigen al'adun su na gargajiya a ranar 8 ga watan ,Maris na shekarar 2021 REUTERS - SERTAC KAYAR
Talla

Manufar ranar wadda aka fara gudanar da ita a shekarar 1908 ita ce tabbatar da ‘yanci da kuma hakkokin jinsin mata a dukkan matakai, baya ga kange su daga barazanar fuskantar cin zarafi ko kaskanci.

Bikin ranar na bana na zuwa ne a daidai lokacin da wani rahoton gamayyar kungiyoyin da ke fafutukar kare hakkin mata ke nuna karuwar cin zarafi da kuma take hakkin matan a sassa daban-daban na duniya.

Kowacce ranar 8 ga watan Maris dubunnan Mata ke gudanar da shagalin bikin murnar zagayowar ranar.
Kowacce ranar 8 ga watan Maris dubunnan Mata ke gudanar da shagalin bikin murnar zagayowar ranar. AFP - THOMAS SAMSON

Amurka ta fara ayyana ranar a shekarar 1909, karkashin jam'iyyar 'yan mazan jiya ta Socialist yayin da aka faro bukukuwan ranar a kasashen Austria da Jamus da kuma Switzerland shekaru biyu bayan matakin na Amurka.

A shekarar 1975 ne aka tabbatar da bikin ranar a hukumance, inda Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranci bikin, kuma taken farko na irin wannan rana a 1996 shi ne "tuna baya da tsara rayuwa ta gaba''.

Wasu mata yayin daukar darasi.
Wasu mata yayin daukar darasi. REUTERS/Danish Siddiqui

Bisa al'ada ranar mata ta duniya kan zamo dandalin tattauna halin da mata ke ciki a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma rayuwar yau da kullum kama daga 'yancinsu a fannonin rayuwa, yayinda a irin wannan lokaci ake shirya mabanbantan gangami don fadakarwa dama yaki da nunawa matan wariya

Taken ranar matan a bana shi ne tabbatar da daidaiton jinsi ta fuskar amfani da fasahar zamani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.