Isa ga babban shafi

Iraqi ta yi Allah wadai da harin bam da Turkiyya ta kai yankin Kurdawa

Shugaban kasar Iraqi Abdel Latif Rashid a yau asabar ya yi Allah wadai da harin bam da dakarun Turkiya suka kai filin jirgin saman Suleimaniyeh na yankin Kurdawan Iraqi, yankin da aka kwashe shekaru ana gwabzawa tsakanin Ankara da mayakan Kurdawan Turkiya na PKK.

Shugaban kasar Iraqi Abdel Latif Rachid,tare da Firaministan sa , Mohamed Chia al-Soudani,
Shugaban kasar Iraqi Abdel Latif Rachid,tare da Firaministan sa , Mohamed Chia al-Soudani, via REUTERS - HANDOUT
Talla

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar Iraqi ta fitar ta bayyana cewa, "An sake maimaita hare-haren sojojin Turkiya kan yankin Kurdawa, na baya-bayan nan shi ne harin bam da aka kai a filin jirgin saman Suleimaniyeh".

A cikin la'antar wadannan hare-haren da ake kaiwa Iraki, muna ba da tabbacin cewa babu wata hujja ta doka ga sojojin Turkiya don bin wannan hanya da ke tsoratar da fararen hula.

Wasu daga cikin mayaka na PKK
Wasu daga cikin mayaka na PKK AFP

Lamarin da ya faru a ranar juma'a a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Suleimaniya, birni na biyu na Kurdawa a arewacin Iraqi, ya zo ne a cikin wani yanayi mai cike da tashin hankali, inda Turkiya ta rufe sararin samaniyarta a farkon watan Afrilu ga jiragen da ke tashi da kuma zuwa wannan filin jirgin.

Ankara ta ba da hujjar wannan matakin ne ta hanyar zargin mayakan Kurdawan Turkiya na jam'iyyar Kurdistan Workers' Party (PKK) da zafafa ayyukansu a wannan fanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.