Isa ga babban shafi

Ba za mu bari Taiwan ta zauna lafiya ba - China

China ta yi gargadin cewa ba zai yiwu Tsibirin Taiwan ya samu zaman lafiya da kuma ‘yancin zama kasa ba a lokaci guda, don haka zabi ya rage wa mahukuntan yankin. 

Wani jirgin yakin China
Wani jirgin yakin China AP - Li Shilong
Talla

Kasar ta Sin ta yi wannan kashedi ne a lokacin da ta kawo karshen atisayen sojin sama da na ruwa da ta shafe kwanaki uku tana yi a kusa da yankin na Taiwan. 

Yayin taron manema labarai da safiyar wannan Litinin, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen China Wang Wenbin, ya ce, muddin ana son a tabbatar da zaman lafiyar Tsibirin Taiwan, to fa ya zama dole a dakile duk wani shiri ko salon bai wa yankin samun damar ‘yancin kai. 

Atisayen sojin da China ta yi dai ya mayar da hankali ne akan dabarun yi wa yankin Taiwan kawanya ta ruwa da ta sama cikin shirin-ko-ta-kwana na afka wa tsibirin idan bukatar hakan ta taso, matakin da daya daga cikin masu magana da yawun rundunar sojin China Kanal Shi Yi ya ce, a shirye suke da su aiwatar, domin wargaza kowanne irin shiri na katsalandan din kasashen ketare, ko tabbatar da samun ‘yancin Taiwan daga Sin. 

A nata bangaren Ma’aikatar Tsaron Taiwan ta ce, jiragen yakin sama guda 70 da kuma manya na ruwa 11 China ta  yi amfani da su wajen yi wa Tsibirin kawanya, a tsawon kwanaki  ukun da dakarun kasar suka shafe suna atisayen, da ya biyo bayan ziyarar da kakakin majalisar wakilan Amurka Kevin McCarthy ya kai yankin cikin makon jiya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.