Isa ga babban shafi

Rashin lafiya ta sa wanda ake zargi da kisan kiyashin Rwanda ba zai fuskanci kuliya ba

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta ce Felicien Kabuga, da ke fuskantar tuhuma bisa zargin yana da hannu a kisan kiyashin Rwanda cewa bashi da isasshiyar lafiyar da zai fuskanci tuhuma.

Felicien Kabuga kenan
Felicien Kabuga kenan AFP/Archivos
Talla

Kotun ta ce za ta yi amfani da wata dokar wacce za ta yi kamanceceniya da shari’ar da ake wa Kabuga mai shekaru 80,amma ba za ta yanke masa hukunci ba.

Alkalai a kotun da ke Hague sun ce Kabuga, wanda ake cece-kuce kan takamaiman ranar haihuwarsa, da wuya ya sake samun isasshiyar lafiya a nan gaba.

An yanke shawarar ne bayan likitoci sun gano cewa Kabuga na fama da cutar mantuwa. Kawo yanzu dai ba a bayyana abin da zai faru da Kabuga wanda ke tsare a gidan yarin kotun ba.

An kama Kabuga a Faransa a shekarar 2020 bayan fiye da shekaru 20 yana tserewa.

Tsohon hamshakin da ke sana’ar shayi ya musanta zargin kisan kiyashi da cin zarafin bil adama.

A watan Satumban bara ne dai aka gurfanar da shi gaban kuliya, inda masu gabatar da kara suka zarge shi da kafa kafafan yada labarai na nuna kyama, wadanda suka bukaci kabilar Hutu da su kashe ‘yan kabilar Tutsi da ke adawa da juna, tare da baiwa mutane makamai.

Masu gabatar da kara sun ce Kabuga ya tallata kalaman nuna kiyayya ta shirye-shiryensa, a gidajen Rediyon da Talibijin na Libre des Milles Collines, da kuma bawa mayakan kabilar Hutu makamai.

Yana da wuya a gurfanar da wadanda ake tuhuma a gaban kotunan duniya da matsalar da ta shafi kwakwalwa.

Kabuga na daya daga cikin wadanda ake zargi da kisan kare dangi a Rwanda na karshe da suka fuskanci shari'a, inda kotun ta yanke wa mutane 62 hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.