Isa ga babban shafi

Japan: Ana shirin garwaya ruwan tashar nukiliya ta Fukushima da ruwan teku

Babban daraktan hukumar kula da samar da makamashin nukliya ta Majalisar Dinkin Duniya (AIEA), Rafaël Grossi, a wannan talatar ya sake ziyartar babbar tashar samar da makamashin nukliya ta Fukushima a kasar Japan, kafin antaya sama da ton milyan daya na  tattacen ruwan tashar nukliyar a cikin tekun pacific.

cibiyar tashar nukiliya ta Fukushima, a kasar Japan.
cibiyar tashar nukiliya ta Fukushima, a kasar Japan. AP - Shohei Miyano
Talla

Kmanin ton miliyan daya da dubu dari uku 1,3 na ruwan da aka shamakance a cibiyar samar da makamashin nukliyar ta Fukushima da ta samu mummunan  hadari, a ranar 11 ga watan maris na 2011 ne, za a saki a cikin ruwan teku.

A ranar talatar da ta gabata ne,  hukumar makamashin nukliya ta duniya (AIEA). Ta tabbatar da cewa watsa wadannan ruwa a cikin teku baya kunshe da hadari ga koshin lafiya ko  ga mahalli.

Sai dai, ko a kasar ta Japan daukar wannan mataki bai gamsar da kuwa ba.

Yau da shekaru 2 ke nan gwamnatin Japan ta yanke shawarar gabatar da neman izini ga hukumar kula da samar da makamashin nukliya ta duniya  (AIEA) domin watsa ruwan a cikin teku, kididiga ta nuna cewa, da dadewa sama da rabin Japanawa ne, ke nuna adawa da matakin, har zuwa wannan lokaci kuma kadan ne suka nuna amincewa da matakin.

Sai dai kuma wani binciken kwakwaf da aka zurfafa ya nuna cewa al’umar Japan sun damu matuka dangane da abinda tattalin arizikin cikin gidan kasar zai girba.

Abin tambaya anan ko Masunta zasu iya sayar da kifi bayn jefa tatacen ruwan ukliyar a  teku   ?  bagaren buda ido kuma ana ganin hakan zai iya jawo raguwar jerin yan yawan buda ido a tashoshin sufurin yankunan arewaci da gabashin tsibirin na Japan

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.