Isa ga babban shafi

Kasar Iraki ta kori jakadan Sweden saboda kona Al-kur'ani mai girma

Iraki ta kori jakadan Sweden jim kadan bayan da masu zanga-zangar suka mamaye ofishin jakadancinta da ke Bagadaza tare da cinnawa wasu sassan ginin wuta.

Masu zanga-zangar sun yi arangama da jami'an tsaro yayin da suke taruwa a kusa da ofishin jakadancin Sweden da ke Bagadaza
Masu zanga-zangar sun yi arangama da jami'an tsaro yayin da suke taruwa a kusa da ofishin jakadancin Sweden da ke Bagadaza REUTERS - AHMED SAAD
Talla

Magoya bayan jagoran mazhabar shi’a na Iraqi Muqtada al-Sadr sun yi kira da a kona ofishin jakadancin Sweden din a ranar Alhamis.

Masu zanga-zangar dai sun fusata ne kan abin da ya ce shi ne karo na biyu da aka kona kur’ani a gaban ofishin jakadancin Iraki da ke Stockholm.

A yayin da masu zanga-zanga a kasar Sweden suka yi ta harbi da kuma lalata wani littafi da suka ce kur’ani ne, said ai ba su kona shi ba kamar yadda suka yi barazanar yi.

Rahotanni daga kasar Sweden na cewa, Salwan Momika dan gudun hijira dan kasar Iraqi mai shekaru 37 a kasar Sweden ne ya shirya lamarin wanda kuma ya kona shafukan kur’ani a gaban babban masallacin birnin Stockholm a ranar 28 ga watan Yuni a lokacin bukukuwan sallah babba.

Lamarin da ya faru a watan da ya gabata ya fusata al’ummar Iraki da magoya bayan al-Sadr, wanda ke matsayin mai ra'ayin kishin jama'a, wanda a baya magoya bayansa suka mamaye majalisar dokokin Iraki, suka mamaye ofishin jakadancin Sweden a Bagadaza.

Wannan aika-aika ya haifar da zanga-zanga da dama a kasashen musulmi kamar yadda gwamnatoci a Iraki, Turkiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Jordan da Morocco suka yi tir da lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.