Isa ga babban shafi

Hukumar Lafiya ta Duniya ta fara razana da yaduwar Korona

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce yawan mutanen da suka kamu da cutar Korona a fadin duniya ya karu da kashi 80 cikin 100 a watan da ya gabata. WHO ta bayyana wannan sabuwar kididdigar ce bayan da hukumar lafiyar ta gano wani  sabon nau’in cutar ta Korona, da ta sanya wa suna Omicron EG.5. 

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus REUTERS - Denis Balibouse
Talla

Cikin watan Mayun da ya gabata ne WHO ta bayyana janye cutar Korona daga nau’ukan cutukan da ke zama barazana ga duniya, sai dai ta yi gargadin cewa kwayar cutar za ta ci gaba da yaduwa gami da rikidewa ko haihuwar wasu nau’ukanta, lamarin da zai haifar da karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar da kuma salwantar rayukan wasunsu. 

Cikin rahoton da ta saba wallafawa a duk mako, hukumar lafiya ta duniya ta ce yawan wadanda suka kamu da Korona daga ranar 10 ga  watan Yuli zuwa ga 6 ga watan nan na Agusta ya kai karin kusan mutane miliyan 1 da rabi a sassan duniya.

Sai dai adadin wadanda cutar ke sanadin mutuwarsu ya ragu da kashi 57 cikin 100 zuwa mutane 2,500 cikin wata guda. 

To amma duk da hakan a iya cewa, tsugunno  ba ta kare ba, domin hukumar ta WHO ta yi gargadin cewa adadin wadanda ke  kamuwa da cutar ta Korona da kuma yawan wadanda suke mutuwa a dalilinta, ya zarce wadanda ake bayyanawa a hukumance, saboda kasashe da  dama ba su tashi tsaye wajen gwaji da aiwatar da  sauran matakan sa ido ba, kamar yadda suka yi a lokacin da annobar ta  barke. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.