Isa ga babban shafi

Taliban: Faransa ta kwashe wasu matan Afganistan da ke fuskantar barazana

Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Faransa Didier Leschi ya shaidawa kamfanin dilancin labaran AFP cewa Faransa ta yi jigilar wasu matan Afganistan biyar da kungiyar Taliban ta yi wa barazana daga Pakistan zuwa birnin Paris.

Wasu dalibai mata kenan da suke kokarin shiga aji, domin zana jarabawa a Kabul na kasar Afganistan, ranar 13 ga watan Oktoba, 2022.
Wasu dalibai mata kenan da suke kokarin shiga aji, domin zana jarabawa a Kabul na kasar Afganistan, ranar 13 ga watan Oktoba, 2022. AFP - WAKIL KOHSAR
Talla

“Bisa umarnin shugaban kasa, za a ba da kulawa ta musamman ga matan da Taliban ke yi wa barazana saboda suna rike da muhimman mukamai a cikin al'ummar Afghanistan, ko kuma suna da kusanci da 'yan kasashen yamma,” in ji Leschi.

Matan sun hada da wata tsohuwar daraktar jami'a, tsohuwar mai ba da shawara ga kungiyoyi masu zaman kansu, tsohuwar mai gabatar da shirye-shirye a wani gidan talabijin, da kuma wata malama a wata makaranta da ke birnin Kabul.

Bayanai sun tabbatar da cewa, daya daga cikin matan na tare da yara uku.

Matan sun kasa barin Afghanistan ta jirgin sama zuwa kasashen yamma bayan da Taliban suka dawo kan karagar mulki a shekarar 2021.

A cewar rahotanni, matan sun gudu zuwa makwabciyar kasar Pakistan inda suka nemi mafaka na wucin gadi. Daga nan ne hukumomin Faransa suka shirya kwashe su.

Da zarar sun isa Faransa, za a yi musu rajista a matsayin masu neman mafaka da kuma ba su gidaje yayin da ake la'akari da aikace-aikacensu na matsayin 'yan gudun hijira, in ji Leschi.

Da zarar sun isa Faransa, za a yi musu rajista a matsayin masu neman mafaka da kuma ba su gidaje yayin da za a ci gaba da la'akari da aikace-aikacensu a matsayin 'yan gudun hijira, in ji Leschi.

Ya kuma ce mai yiyuwa ne a sake maimaita irin wannan Shirin na gudun hijira ga sauran matan Afganistan masu irin wannan bayanin matsala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.