Isa ga babban shafi

China ta kaurace wa taron G20 a India

Shugaban Amurka Joe Biden da sauran shugabannin kasashen G20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya sun hallara a birnin New Delhi na India domin gudanar da taronsu na shekara-shekara a daidai lokacin da suke fama da rarrabuwar kawuna, yayin da shugaban China Xi Jinping ya kaurace wa taron.

Taron kasashen g20 a birnin New Delhi na China.
Taron kasashen g20 a birnin New Delhi na China. AP - Dar Yasin
Talla

Shugaban China Xi Jinping da ya kaurace wa taron ya diga ayar tambaya kan muhimmancin kungiyar kasashen na G20, kodayake ya aika firaministansa, Li Qiang domin wakiltar sa.

Babu dai wani gamsasshen uzuri da za a amince da shi a hukumance na rashin halartar shugaba Xi na China.

Shugaban Amurka Joe Biden a wurin taron G20 a India.
Shugaban Amurka Joe Biden a wurin taron G20 a India. AP - Alex Brandon

An dai kirkiri kungiyar ce da zummar nazartar matsalolin tattalin arziki da ke addabar duniya, amma har yanzu mambobinta na ci gaba da samun rashin jituwa a shekarun baya-bayan nan kan batutuwa da dama.

India da ke karbar bakwancin taron a bana, na kokarin ganin yadda za ta jagoranci cimma yarjejeniya kan wasu batutuwa masu cin-rai  da suka hada da yakin Ukraine da matsalar sauyin yanayi da kuma jagorancin duniya.

Kasashen na G20 na fama da tarin rashin jituwa a tsakaninsu.
Kasashen na G20 na fama da tarin rashin jituwa a tsakaninsu. © Aijaz Rahi / AP

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya gargadi shugabannin kasashen duniyar kan cewa, rashin jituwarsu na rura wutar rikice-rikice tare da wargaza amanar da mutane suka danka musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.