Isa ga babban shafi

Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu a Turai

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa a tsakiyar birnin London a Asabar din nan, inda su ke bukatar a gaggauta tsagaita wuta a mummunan rikicin da ake gwabzawa tsakanin Isra’ila da Hamas a Gaza, da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Masu zanga-zangar ggoyon bayan Falasdinawa a birnin London, yau Asabar 28 Oktoba 2023.
Masu zanga-zangar ggoyon bayan Falasdinawa a birnin London, yau Asabar 28 Oktoba 2023. REUTERS - SUSANNAH IRELAND
Talla

Wannan ne dai karshen mako na uku a jere da ake gudanar da irin wannan zanga-zanga a birnin London, tun bayan faro rikicin a farkon wannan watan.

Zanga-zanagar ta yau Asabar dai na zuwa ne, bayan da Isra’ila ta kara matsa kaimi wajen kai hare-hare a yankin Gaza a ranar Juma’ar da ta gabata.

Masu zanga-zangar sun ta rera wakokin goyon bayan Falasdinu, da nuna goyon baya wajen samun cin gashin kan kasarsu tare kuma da dakatar da hare-haren da Isra’ila ke kai musu.

Daya daga cikin masu zanga-zangar Dani Nadiri, ya ce bukatar neman tsakaita kai hare-hare da fara ministan Burtaniya Rishi Sunak ya mika bata wadatar ba, abinda ya fi shi ne kawo karshen rikicin baki daya.

Zanga-zanga a Paris

Har wayau, duk da haramta zanga-zangar da aka yi a birnin Paris daruruwan mutane ne suka fito don nuna goyon bayanzu ga Falasdinu.

Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a Paris yau 28 Oktoba 2023.
Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a Paris yau 28 Oktoba 2023. © Bertrand Guay / AFP

Daga cikin masu zanga-zangar har da zababbun ‘yan siyasa, inda mataimakin magajin garin Corbeil-Essonnes, Elsa Toure wacce ta bukaci a dakatar da kashe mata da kananan yara da ma magidanta da ake yi.

Zanga-zanga a Istanbul

Shima shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan, ya jagoranci wata zanga-zanga a yau Asabar a babban birnin kasar Istanbul, wacce ta samu halartar mutane miliyan daya da rabi, inda ya ce kasashen yamma ke da alhakin kai hare-haren da Isra’ila ke yi a yankin Gaza.

Masu zanga-Sanza a babban birnin Turkiya Istanbul, yau 28 ga watan Oktoba 2023.
Masu zanga-Sanza a babban birnin Turkiya Istanbul, yau 28 ga watan Oktoba 2023. © Dilara Senkaya / Reuters

Ya ce akullum suna zubba hawaye kan jinin ‘yan Ukraine da ake zubarwa, amma kuma sun rufe idanunsu kan na Falasdinawa da ke kwarara.

Tsokacin Saudiya

Saudiya ta yi Allah wadai da hare-hare ta kasa da Isra’ila ke kaiwa yankin Gaza, lamarin da ta bayyana a matsayin wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Wannan gargadi dai na zuwa ne bayan da kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila Daniel Hagari ya ce a daren jiya Juma’a, sojojinsu sun ci gaba da kutsawa ‘yankin Gaza ta kasa.

Hukumomin Isra’ila sun ce hare-haren da Hamas ta kai a cikin kasar a ranar 7 ga wannan watan, yayi sanadiyar mutuwar mutane dubu daya da dari 4.

Ita kuwa ma’aikatar kula da kiwon lafiyar Falasdinu ta ce hare-haren da Isra’ila ta kaddamar a Gaza, sun kashe fararen hula dubu 7 da dari 703, daga cikin wancan adadi akwai yara sama da dubu 3 da dari 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.