Isa ga babban shafi

Kyamar Yahudawa na kara fitowa fili saboda harin da ta ke kaiwa Gaza

Mutane a kasashen duniya na ci gaba da fitowa fili suna Allah wadai da Isra’ila tare da nuna kyama ga Yahudawa, saboda yakin da ta kaddamar a zirin Gaza.

Yadda wasu aka gudanar da zanga-zanagar neman Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare kan Falasdinawa a Gaza.
Yadda wasu aka gudanar da zanga-zanagar neman Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare kan Falasdinawa a Gaza. AFP - KENA BETANCUR
Talla

Sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa yankin a zirin Gaza, bayan harin da Hamas ta kai kudancin kasar a ranar 7 ga watan Okotoban nan, kalaman nuna kyamar Yahudawa na kara yawaita a sassa daban-daban na duniya.

A kasashe irin su Amurka da Burtaniya da Faransa da Jamus da kuma Afrika ta Kudu, al’amarin a bayyane ya ke game da yadda aka samu karuwar  kalaman nuna kyamar Yahudawa a yanzu, idan aka kwatanta da yadda aka samu a irin wannan lokaci a shekarar da ta gabata.

A birnin Los Angeles na Amurka, wani mutum yayi ta yin kururuwar cewar a kashe Yahudawa, a birnin Londan, nan ma an ga wasu yara mata a filin wasa na cewa Yahudawa na doyi, haka a kasar China, anga rubuce-rubucen da ke kwatanta Yahudawa da kwari ko masu shan jini ko kuma macizai, abinda ke cin kasuwa a shafukan sada zumunta.

Anthony Adler, mai shekaru 62 a duniya, ya ce wannan shi ne lokaci mafi ban tsoro da Yahudawa suka tsinci kansu a ciki tun bayan yakin duniya na biyu.

Adler wanda ke da makarantun ‘ya’yan Yahudawa 3 a Golders Green, wani yankin da ke da yawan Yahudawa a kusa da birnin London, ya ce sun rufe makarantun na wucin gadi tare da tsaurara matakan tsaro, saboda tsoron kar a kai musu hari.

“Babban abin tsoro shi ne za a iya kai wa garuruwanmu harin ba-zata, kan iyalanmu da ‘ya’yanmu.”

Game da abubuwan da ke faru wa na nuna kyamar Yahudawa, galibi sun shafi zage-zage da barazana da rubuce-rubuce da lalata kayayyakin Yahudawa ko wuraren kasuwanci ko na ibada da dai sauransu.

Wadannan dai na daga cikin hanyoyin da wasu ke nuna fushinsu kan irin munanan hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin Gaza, wanda yayi sanadiyar mutuwar dubban Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.