Isa ga babban shafi

Cameron ya zama Ministan Harkokin Wajen Birtaniya

Tsohon Firaministan Birtaniya, David Cameron ya zama ministan harkokin wajen kasar, yayin da gwamnatin masu ra’ayin mazan jiya ta gudanar da sauye-sauyen ministoci, ciki kuwa har da sallamar ministan harkokin cikin gida ta kasar Suella Braveman. 

David Cameron
David Cameron © Suzanne Plunkett/Reuters
Talla

Cameron, wanda ya jagoranci Birtaniya tsakanin shekarar 2010 zuwa 2016, an nada shi cikin ministocin Rishi Sunak, yayin da firaministan ya fusata da sallamar Braveman, bayan ta caccaki jami’an ‘yan sanda da yin sassauci ga masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. 

Bayanai sun tabbatar da cewa, tuni aka maye gurbinta da James Cleverly, wanda ya taba rike mukamin Ministan Harkokin Wajen Kasar. 

Nadin David Cameron ya zo da mamaki, musamman ga masana a bangaren siyasa, la’akari da irin mukamin da ya rike a baya. 

Yana da wuya wanda ba dan majalisa ba ya samu babban mukami na gwamnati, kuma an kwashe shekaru da wani tsohon firaminista ya rike mukamin a majalisar ministoci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.