Isa ga babban shafi

Kotun Kolin Birtaniya ta dakile shirin tasa keyar baki zuwa Rwanda

Kotun Kolin Birtaniya ta yi watsi da shirin gwamnatin kasar na tura bakin haure zuwa Rwanda, a wani mataki da ke zama babban koma-baya ga Firaminista Rishi Sunak. 

Wasu bakin haure a Birtaniya.
Wasu bakin haure a Birtaniya. © AFP - Ben Stansall
Talla

Alkalan Kotun Kolin Birtaniyan biyar sun goyi bayan hukuncin kotun daukaka kara ba tare da wata hamayya ba matakin ya saba wa manufar Birtaniya a karkashin yarjejeniyoyin kasa da kasa. 

A cikin daftarin hukunci mai shafuka 56, alkalan sun amince da hukuncin da wata karamar kotu ta yanke a watan Yuni cewa Rwanda na fuskantar kasadar mayar da masu neman mafaka da 'yan gudun hijira tilasta musu zuwa kasarsu da watakila suke fuskantar tsangwama. 

Gwamnatin Sunak ta dage cewa shirin wani muhimmin mataki ne na rage kwararar bakin haure da ke ratsa teku cikin kananan jiragen ruwa domin shiga Turai ba bisa ka'ida ba, batun zai da zai dauki hankali a babban zabe mai zuwa. 

A watan Yunin bara, an shirya tawagar ‘yan cin rani na farko da zai nufi kasar Rwanda, daf da shirin tashi ne, wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Turai ta hana fitar da bakin, ta mai cewa ya saba dokokin duniya. 

Da ma masu adawa da shirin na tura baki Rwanda na sukar lamirin a matsayin zalunci. 

Tuni Rwanda ta nuna rashin jin dadinta kan hukuncin kotun kolin ta Birtaniya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.