Isa ga babban shafi
TARON G20

Jamus ta sha alwashin zuba jarin Yuro biliyan 4 ga kasashen Afirka

Kasar Jamus ta sha alwashin zuba jarin Yuro biliyan hudu wajen samar da makamashi wanda baya gurbata muhalli a nahiyar Afirka daga nan zuwa shekarar 2030.

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz  kenan.
Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz kenan. POOL/AFP
Talla

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya ce ya kamata kasashen nahiyar su amfana da arzikin albarkatun kasarsu ta hanyar sarrafa musu shi.

Shugaban na Jamus wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudana a taron G20 a birnin Berlin, be bayyana irin ma’adanan da za su yi amfani da su wajen samar da makamashi ga nahiyar ba.

Scholz ya ce kasar Jamus za ta kasance babbar abokiyar huldar kasashen Afirka ta fuskar samar da ci gaba, musamman wajen yakar matsalar dumamar yanayi da ke addabar nahiyar.

Ko da aka tambayI shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki, kan tasirin da kasar China ke da shi a nahiyar, Sai ya ce kofa a bude take ga duk kasar da take sha’awar hulda da Afirka.

Sai dai kasashen Afirka, sun jima suna korafin cewa sun gaji da romon bakar da kasashen Turai ke musu na samar da ci gaba mai dorewa, amma kai tsaye China ke aiwatar da duk wani aikin ci gaba da ta yi musu alkawari ba tare da wasu sharudda masu tsauri ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.