Isa ga babban shafi

Kasashen Turai za su samar da dokokin sa ido kan fasahar AI

Faransa Jamus da Italiya sun cimma matsaya kan samar da dokokin sa ido, da kuma fayyace yadda za a rika amfani da fasahar nan ta kimasa wa na’ura basirar dan adam, wadda aka fi sani da ‘Artificial Intelligence’ a turance. 

Tambarin kamfanin kamfanin Google kenan da kuma OpenAi da aka dauka a kasar Faransa.
Tambarin kamfanin kamfanin Google kenan da kuma OpenAi da aka dauka a kasar Faransa. AFP - LIONEL BONAVENTURE
Talla

 

Cikin takardar bayan taron da suka fitar a karshen mako, kasashen uku sun bayyana cewa dokokin da za su kafa za su mayar da hankali ne akan yadda ake sarrafa fasahar da kimsa wa na’ura basirar dan Adam ne, ba kokarin dakile kimiyyar da ta haifar da cigaban fasahar ba, kamar yadda wasu ke tunani. 

Ana dai sa ran matsayar da kasashen na Faransa, da Jamus da kuma  Italiya suka cimma, ta share fagen fara tattaunawa tsakanin sauran kasashen Turai, kan makomar fasahar da sanya na’ura ko mutun-mutumi basirar dan  Adam. 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ma’aikata kimanin 500 na fitaccen kamfanin OpenAI da yayi fice wajen bincike kan fasahar kimsa wa na’ura basirar dan Adam suka yi barazanar ajiye ayyukansu, da kuma yunkurin sauya sheka zuwa kamfanin kera kwamfuta da sauran fasahohinta na  Microsoft. 

A halin yanzu dai kamfanin na Microsoft ya kulla yarjejeniya da tsohon shugaban kamfanin OpenAI, Sam Altman, da mataimakinsa Greg Brockman, bayan da aka kore su daga bakin aiki a bisa zarginsu da zurfafa bincike fiye da kima da kuma kokarin aiwatar da gwaje-gwajen amfani da fasahar AI ba tare da  damuwa da hatsarin da ke tattare da hakan ba, zargin da daruruwan kananan ma’aikatnsu suka musanta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.