Cutar sarkewar numfaashi da ta bulla a China ba ta kai Covid-19 ba - WHO
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce, cutar sarkewar numfashi da aka sake samun bullarta a kasar China, ba ta kai cutar Covid-19 da ke saurin yaduwa ba.
Wallafawa ranar:
WHO ta ce har yanzu ba a kai ga gano kwayoyin cutar da suka haifar da irin wannan cuta ba.
Maria Van Kerkhove, mukaddashiyar daraktan sashen kula da cutuka masu yaduwa ta WHO, ta ce karuwar adadin mutanen da ke fama da wannan cuta da ake samu, baya rasa nasaba da raunin garkuwar jiki da kananan yara ke da shi.
Kakakin ma’aikatar lafiya ta kasar China, Mi Feng, ya ce yaduwar cutar sarkewar numfashin da ake samu ga kananan yara, na da nasaba ne da wasu kwayoyin cuta masu kamanceceniya da mura da suke fama da ita.
A makon jiya ne WHO ta bukaci kasar China da ta yi mata cikakken bayani, kan cutar sarkewar numfashin da aka samu labarin cewa tana kama kananan yara, yayin da duniya ta shiga rudani domin fargabar abin da ka iya maimaita kansa na cutar Covid-19.
China da WHO sun fuskanci tambayoyi kan sahihancin rahoton da aka samu game da cutar da ta bulla a Wuhan wato inda Covid-19 ta samo asali a karshen shekarar 2019.
Sai dai rahoton da WHO ta fitar ya tabbatar da cewa, wannan cutar ba za a kira ta a matsayin annoba ba, kamar yadda cutar sarkewar numfashi ta Covid-19 ta addabi duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu