Isa ga babban shafi

Majalisar dinkin duniya na bukatar dala biliyan 46 don ayyukan jin kai a badi

Majalisar dinkin duniya ta ce tana bukatar akalla dala biliyan 46.5 don ci gaba da aikin tsamo fiye da mutane miliyan 180 da ke rayuwa cikin tsakananin yunwa  a duniya a 2024.

Samar da zaman lafiya da fatattakar yunwa sune manyan abubuwan da majalisar dinkin duniyar zata mayar da hankali a badin.
Samar da zaman lafiya da fatattakar yunwa sune manyan abubuwan da majalisar dinkin duniyar zata mayar da hankali a badin. AFP - YUKI IWAMURA
Talla

Sanarwar majalisar na zuwa ne a da-dai lokacin da duniya ke fama da mastin tattalin arziki, yayin da yake-yake, sauyin yanayi da kuma afkuwar bala’o’i ke sake nutsa mutane cikin yunwa.

Yayin da hankalin duniya yanzu haka ya karkata kan yakin Isra’ila da Gaza, majalisar dinkin duniya ta ce gabas ta tsakiya, Sudan da Afghansitan na cikin yankunan da ya kamata duniya ta mayar da hankali akan su, la’akari da halin kunci da jama’ar su ke fama da shi.

Miliyoyin mutanen ne ke fama da tsananin yunwa a Sudan
Miliyoyin mutanen ne ke fama da tsananin yunwa a Sudan cds/AFP

Sai dai kuma kididdiga ta nuna duk da yadda ake samun karuwar mutanen dake neman taimako, adadin kudaden da majalisar ke bukata a badin bai kai wanda ta yi amfani da su a bana ba, sakamakon karancin masu baiwa majalisar taimakon kudade da aka samu.

Ayyukan da majalisar dinkin duniyar kan yi da irin wadannan kudade sun hadar da ceton rayukan jama’a, fatattakar yunwa, kare kananan yara, dakile barkewar cututtuka da kuma samar da matsugunai ga mutanen da rikici ya raba da muhallan su.

A bana dai majalisar ta bukaci a tara mata akalla dala biliyan 56.7, amma ta kare da samun kaso 35 kachal na abinda ta bukata, kudi mafi karanci kenan da ta samu cikin shekaru masu yawa da take karbar kudade daga hannun masu bada tallafi.

Majalisar dinkin duniya na fatan tsamo mutane sama da miliyan 180 daga yunwa a badi
Majalisar dinkin duniya na fatan tsamo mutane sama da miliyan 180 daga yunwa a badi © SIMON MAINA / AFP

Bayan samun wadannan kudade majalisar dinkin duniyar itama ta kan baiwa kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa da ke taimakawa mutane sama da miliyan 120 tallafi.

La’akari da yadda lamura ke tafiya yanzu haka, da yadda yake-yake ke gudana a tsakanin kasashe akwai hasashen a badi ma majalisar dinkin duniyar ta kasa samun adadin kudaden da ta bukata.

Shekarar 2010 ce dai shekara mafi muni da majalisar dinkin duniyar ta gani a fannin tara kudaden taimako, inda ta gaza tara ko da kaso 10 ciki 100 na abinda ta bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.