Isa ga babban shafi

Amurka da Birtaniya sun kara lafta wa Hamas takunkumai

Amurka da Birtaniya sun sanar da lafta wa Hamas sbbin takunkumai sakamakon harin da kungiyar ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban, inda aka samu salwantar rayuka.

Wasu daga cikin mayakan Hamas
Wasu daga cikin mayakan Hamas © AFP
Talla

Ma'aikatar Baitul Malin Amurka ta ce, wannan mataakin ya shafi manyan jami'an da ke ruruta manufar ta'addacin Hamas ta hanyar wakiltar manufofin kungiyar a kasashen ketare tare da kula da asusunta.

Tun bayan harin na Oktoba da kungiyar ta kaddamar da ya kashe kimanin mutane dubu 1 da 200 akasarinsu fararen hula, tare da garkuwa da mutane 240, Amurka ke matsin lamba kan mayakan. 

Baitul Mali Amurka ya ce, Hamas ta ci gaba da dogaro kan gungun wasu jami'ai da aminansu da alamu ke nuna cewa, suna nema wa kungiyar tallafin kudi don ci gaba da gudanar da ayyukanta a Zirin Gaza.

Takunkuman sun shafi sama da gomman jami'an Hamas da masu taimaka musu da suka hada da Isma'il Barhum da ke zauna a Gaza, wanda aka ce shi ne shugaban kula da kudade a yankin, inda kuma yake tattaro wa kungiyar kudin tallafi daga kasashen duniya don zuba wa a asusun ma'aikatar kudi ta Hamas din.

Birtaniya ta ce, Hamas za ta iya rasa makomarta a Gaza, inda Sakataren Harkokin Wajen Kasar, David Cameron ya ce, 

Takunkuman da aka lafta wa Hamas da mayakan jihadi a Falasdinu za su ci gaba da datse musu hanyoyin samun kudaden shiga, sannan su zama saniyar ware.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.