Isa ga babban shafi

Dole kasashe su yi shirin tunkarar annobar da ka iya bulla- WHO

Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta bukaci kasashe su yi shirin ko ta kwana don tunkarar duk wata annobar cuta da ka iya barkewa a nan gaba, dai dai lokacin da duniya ke kawo karshen annobar Covid da ta haddasa dimbin asarar rayuka da dukiyoyi tsawon shekaru 3.

Sakatare Janar na hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Sakatare Janar na hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus. © AFP
Talla

Darakta Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a jawabinsa na karshen shekara ta bidiyo, ya ce akwai bukatar hada hannu tsakanin kasashe wajen samar da wata yarjejeniya da za ta zama tunga ga duk wata annoba da ka iya bulla a kowanne lokaci.

A cewar Dr Tedros, shekarar 2023 za ta zama wani bigire da zai samar da sauyi a salon yaki da matsalolin da bangaren lafiya ke fuskanta da zai kange jama’a daga tsintar kansu a wahalhalu ko da bayan bullar wata annobar cuta a nan gaba.

Shugaban na WHO wanda ya kuma nemi kasashe su taimaka wajen tallafawa Gaza da ke fuskantar tarin matsalolin durkushewar bangarorin lafiya sakamakon hae-haren Isra'ila da kuma yiwuwar fuskantar bullar cutuka sakamakon karancin abinci da rashin tsaftataccen ruwan sha, ya ce wajibi ne kowacce kasa ta kasance cikin shirin ko ta kwana don tunkarar duk wata barazanar annobar cuta da ka iya afka mata.

A watan Mayun shekarar nan, WHO ta sanar da kawo karshen annobar Covid-19 wadda aka samu bullarta tun cikin watan Disamban 2019 a yankin Wuhan na tsakiyar China.

A cewar Tedros Adhanom bayan nasarar kawar da Covid, a bangare guda anyi nasarar kawo karshen annobar mashako ta mpox yayinda aka samar da sabbin rigakafin Malaria da Dangue da kuma Sankarau, bugu da kari kasashen Azerbaijan, Belize da Tajikistan suka sanar da murkushe Malaria baki daya.

Shugaban na WHO ya ce akwai bukatar shiryawa tsaf don kaucewa irin bannar da Covid ta haifarwa duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.