Isa ga babban shafi

Kasashe fiye da 50 za su gudanar da manyan zabukansu a cikin 2024

Fiye da kasashe 50 ne ke shirin gudanar da manyan zabukansu cikin shekarar nan ta 2024, adadin da ke wakiltar fiye da rabin yawan al'ummar duniya, wanda ke matsayin karon farko da irin hakan ke faruwa a tarihin duniya.

Taiwan ce ta farko da za ta gudanar da zabe a jerin kasashen 50.
Taiwan ce ta farko da za ta gudanar da zabe a jerin kasashen 50. © AP - ChiangYing-ying
Talla

Daga Rasha zuwa Taiwan da Birtaniya kana India da kuma El Salvador da Afrika ta kudu wadanda dukkaninsu za su gudanar da zabukan shugaban kasa da ‘yan majalisu, akwai fargabar matsaloli masu alaka da take hakkin dan adam su iya kawo nakasu a kasashen.

A wasu kasashen kuwa akwai yiwuwar zabukan su kasance ba yabo ba fallasa musamman tsakanin gwamnatocin da ke mulki da jam’iyyun adawar da ke neman maye gurbinsu.

Zaben da zai fi jan hankali shi ne na Amurka, inda za a kara tsakanin shugaba mai ci Joe Biden da tsohon shugaban kasar Donald Trump wanda kujerar ta subuce masa a shekarar 2020.

'Yan takarar neman shugabancin Amurka Donald Trump da Joe Biden yayin muhararsu ta farko
'Yan takarar neman shugabancin Amurka Donald Trump da Joe Biden yayin muhararsu ta farko REUTERS/Brian Snyder
Taiwan za ta gudanar da nata zaben a ranar 13 ga watan nan na Janairu inda ‘yan takara za su fafata don neman kujerun majalisa 113 dai dai lokacin da yankin mai kwarya-kwaryar ‘yanci ke fuskantar matsin lamba daga China.

Tun a Litinin din makon jiya Bangladesh ta gudanar da nata zaben wanda ya bai wa Firaminista Sheikh Hasina damar ci gaba da jagorancin kasar matsayin shugaba mace ta farko mafi dadewa a kan kujerar mulki a tarihin duniya.

India da ke matsayin kasa mafi yawan jama’a, akwai yiwuwar dakile bangaren adawa a nata zaben lura da yadda jam’iyyar Firaminista Narendra Modi ta BJP ke neman wa’adi na 3 bayan murkushe bangaren adawa.

Jam'iyyar BJP na ci gaba da murkushe bangaren adawa a India.
Jam'iyyar BJP na ci gaba da murkushe bangaren adawa a India. AP - Rajesh Kumar Singh

Shugaba na gaba da ke neman tazarce cikin shekarar nan shi ne na El Salvador Nayib Bukele, wanda ke ci gaba da samun goyon baya tun bayan nasarar murkushe matsalar ‘yan daba a sassan kasar inda a watan Fabarairu mai zuwa ke shirin neman sabon wa’adin mulkin kasar bayan kammala zagaye 2 na mulkin kasar.

A watan Yuni mai zuwa ne al’ummar Mexico za su fita runfunan zabe don kada kuri’a a zaben da ke shirin samarwa kasar shugaba mace ta farko a tarihi.

A ranar 14 ga watan Fabarairu mai zuwa ne al’ummar Indonesia za su zabi wanda zai maye gurbin shugaba Joko Widodo a zaben da za a fafata tsakanin ministan tsaro Prabowo Subianto da kuma tsohon gwamnan Java Ganjar Pranowo.

Shugaba Joko Widodo ya kawo karshen wa'adin mulkinsa a bana.
Shugaba Joko Widodo ya kawo karshen wa'adin mulkinsa a bana. AP - Muchlis Jr
Haka zalika Pakistan za ta gudanar da zaben ‘yan Majalisu a ranar 8 ga watan Fabarairu dai dai lokacin da tsohon Framinista Imran Khan ke fuskantar haramcin shiga zaben.

Kasashe 27 mambobin kungiyar EU za su kada kuri’a don zaben wakilansu a Majalisar kungiyar zaben da ake ganin zai banbanta matuka da makamancinsa na shekarar 2019 lura da yadda aka samu rarrabuwar kai tsakanin mambobin kungiyar bayan fara yakin Rasha da Ukraine.

Kasashe 27 mambobin EU ke shirin kada kuri'a cikin shekarar nan.
Kasashe 27 mambobin EU ke shirin kada kuri'a cikin shekarar nan. AP - Yves Logghe

Rasha na shirin gudanar da nata zaben a cikin watan Maris din shekarar nan, zaben da shugaba Putin zai sake neman karin wa'adin ci gaba da jagorancin kasar. 

Shugaba Vladimir Putin na neman sabon wa'adin mulkin kasar.
Shugaba Vladimir Putin na neman sabon wa'adin mulkin kasar. AP - Alexei Druzhinin

A nahiyar Afrika, bayan fuskantar juyin mulki a kasashen yammacin nahiyar har sau 8 daga 2020 zuwa yanzu, Afrika ta kudu da Senegal ne kasashe ‘yan gaba gaba da za su gudanar da zabe a bana kana Sudan ta kudu wadda ta jinkirta zabenta na bara.

A bangare guda Belarus na Shirin gudanar da nata zaben a inda shugaba Alexandre Lukashenko babban abokin Vladimir Putin ke neman sabon wa’adin mulki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.