Isa ga babban shafi

Sarkin Ingila Charles ya kamu da cutar sankara

Sarkin Ingila, mai martaba Charles na III ya kamu da cutar kansa kamar yadda sakamakon binciken likitoci ya nuna, yayin da tuni ya fara karbar magani kamar yadda fadar Buckingham ta bayanna a wannan Litinin.

Sarkin Ingila, Charles na III
Sarkin Ingila, Charles na III © Alberto Pezzali / AP
Talla

 

 

Fadar ta ce, cutar ta kansa ba ta da alaka da maganin da aka yi wa sarkin na wata 'yar kamarar cutar mafitsara a kwana-kwanan nan. Kodayake fadar ba ta sanar da nau'in kansar da sarkin mai shekaru 75 ke fama da ita ba a yanzu.

 

A yau mai martaba ya fara karbar magani daki-daki, inda likitoci suka ba shi shawarar da ya dage duk wani aikin da ya shafi fuskantar jama'a.  Mai martabar zai ci gaba da gudanar da harkokin kasa da kuma sanya hannu kan takardu kamar yadda ya saba. Inji fadar.

 

A cewar fadar ta Buckingham, sarkin ya zabi ya fallasa sakamkon gwajin da aka yi masa ne ga jama'a domin hana yaduwar jita-jita, tare da fatan hakan zai taimaka wa al'umma su fahimci yanayin da mutanen da ke fama da kansa a sassan duniya ke ciki.

 

A cikin watan Satumban 2022 ne, Charles ya zama sarkin Ingila bayan mahaifiyarsa, Sarauniya ELizabeth ta II ta mutu tana da shekaru 96.

Tuni manyan 'yan siyasar Birtaniya suka fara aikewa da sakon nuna goya baya ga sarkin na Ingila, inda suke fatan zai samu cikakkiyar murmurewa cikin kankanin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.