Isa ga babban shafi

Hukumomin haraji sun daskarar da asusun babbar jam'iyyar adawar India

Babbar jam'iyyar adawa ta Congress a Indiya a yau Juma'a ta sanar da cewa hukumomin haraji sun rufe asusun ajiyarta na banki, makonni kafin sanarwar da ake sa ran za a yi na zaben kasa mai zuwa.Kakakin jam'iyyar Congress Ajay Maken ya ce "An gaya mana cewa an daskarar da asusun babbar jam'iyyar adawa ta India" a wani bangare na binciken da aka yi na dawo da harajin da ta yi a baya.

Firaministan India  Narendra Modi a New Delhi
Firaministan India Narendra Modi a New Delhi AP - Dar Yasin
Talla

Ma'aikatar haraji ta India ta bukaci a biya Rupee biliyan 2.1 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 25.3 a wani bangare na binciken kudaden harajin jam'iyyar na shekara ta 2018 zuwa 2019.

Nitish Kumar, Minista kuma shugaban yankin Bihar.
Nitish Kumar, Minista kuma shugaban yankin Bihar. AFP - MONEY SHARMA

Da yake tabbatar da cewa jam’iyyar ba ta yi wani abu ba don tabbatar da irin wannan takunkumin, Ajay  Maken ya yi la’akari da cewa wannan tsari na da nufin jefa jam’iyyar cikin wahala kafin zabe.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da ‘yan adawa sun zargi gwamnatin Firaminista Narendra Modi da yin amfani da jami’an tsaro wajen azabtar da ‘yan adawa.

Magoya bayan jam'iyyar  BJP a India
Magoya bayan jam'iyyar BJP a India REUTERS - AMIT DAVE

Shugaban jam'iyyar Congress Rahul Gandhi, wanda shi ne shugaban daular da ta mamaye siyasar India tsawon shekaru da dama, an same shi da laifin bata masa suna a bara bayan wani dan jam'iyyar Firaminista Modi ya shigar da kara.

Daurin shekaru biyu a gidan yari ya hana shi shiga majalisar har sai da aka dakatar da hukuncin kan daukaka kara, lamarin da ya kara nuna damuwa game da mutunta tsarin dimokuradiyya a kasar da ta fi yawan al'umma a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.