Isa ga babban shafi

Manoma a India na zanga-zanga kan tsadar kayan noma

Manoma a India sun fantsama kan titunan birnin Delhi tare da gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar takin zamani da sauran kayan noma da ke barazana ga aikin nasu.

Dubban manoma a India lokacin da suke zanga-zanga
Dubban manoma a India lokacin da suke zanga-zanga © Reuters - Anushree Fadnavis
Talla

 

Bayanai sun ce manoman sun yi amfani da manyan motocin tarakta wajen datse hanyoyin shiga da fita birnin na Delhi don ankarar da gwamnati game da koken su.

 

 

Duk da cewa jami’an ‘yan sanda sun yi ta jefawa manoman hayaki mai sa hawaye, amma hakan bai hana su ci gaba da jerin gwanon ba.

Manoman na bukatar gwamnati ta samar da hanyoyin saukaka farashin takin zamani da kuma irin shuka tare da tsayar da farashi ba tare da barin sa a hannun ‘yan kasuwa  ba.

Haka kuma manoman suna bukatar gwamnati ta sake duba tsarin basu bashi da kuma yadda ake biya, a cewar su tsarin kwata-kwata baya taimakon su.

 

 

 

 

Kungiyar manoman ta ce bayan wannan zanga-zanga zata yi ganawa da gwamnati a hukumance don tabbatar da cewa kasar ta ci gaba da rike kambunta matsayin ta daya wajen samar da auduga a duniya, yayin da take ta biyu wajen samar da sukari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.