Isa ga babban shafi

Aikin kwashe shara ka iya lakume dala biliyan 270 a duniya idan ba'a yi hattara ba-MDD

Majalisar Dinkin Duniya tace a shekarar da ta gabata al’umma sun tara sharar da yawanta ya kai tan biliyan 2 da miliyan 300, a fadin Duniya, wadda adadin ka iya karuwa da kaso biyu cikin uku nan da shekarar 2050.

Wannan dai na faruwa duk da yadda wasu ke ganin sharar ka iya komawa dukiya idan aka sarrafata yadda ya dace
Wannan dai na faruwa duk da yadda wasu ke ganin sharar ka iya komawa dukiya idan aka sarrafata yadda ya dace REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Majalisar ta kuma yi gargadin cewa hakan zai kawo tasgaro ga harkokin tattalin arziki da muhalli da kuma kiwon lafiyar al’ummar Duniya.

Wani sabon rahoto da hukumar kula da muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar bayan gudanar da bincike, ya nuna fargabarsa game da yiwuwar karuwar matsalar gurbacewar yanayi musamman a yankunan da al’umma suka saba zubar da shara tare da kone ta a kofar gidajen su.

Binciken ya biyo bayan wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar a shekarar 2018, cewa nan da shekarar 2050, sharar da al’umma za su rinka tarawa a Duniya duk shekara za ta kai tan biliyan 3 da miliyan 400.

Kazalika rahoton hukumar Muhallin, yace wannan lamari ka iya yin kamari a wuraren da ake da masana’antu da ke fitar da sinadarai masu bin hanyoyin ruwa da iska.

A cewar hukumar matukar, kasashen Duniya ba su dauki matakan gaggawa kan wannan matsala da ta tunkaro su ba, akwai yiwuwar adadin sharar da ake tarawa ya karu zuwa tan Biliyan 3 da miliyan 800, wanda hakan ya zarta adadin yadda aka yi hasashe a baya, ta kara da cewa matukar ana son magance matsalar a duk shekara sharar sai ta lakume Dalar Amurka Biliyan 270.

A wannan makon ne Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da taron Muhalli, a Nairobi babban birnin kasar Kenya, domin lalubo hanyoyin magance matsalolin sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.