Isa ga babban shafi

Putin ya gargadi kasashen yamma kan yunkurin girke dakarun NATO a Ukraine

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya gargadi kasashen yammaci game da hadarin girke dakarun kungiyar tsaro ta NATO a Ukraine yana mai cewa matakin tamkar bude babin yakin nukiliya ne a tsakaninsu.

Shugaba Vladimir Putin yayin gabatar da jawabin kasa gaban Majalisa da kusoshin gwamnatinsa kwanaki kalilan gabanin zaben kasar.
Shugaba Vladimir Putin yayin gabatar da jawabin kasa gaban Majalisa da kusoshin gwamnatinsa kwanaki kalilan gabanin zaben kasar. REUTERS - Evgenia Novozhenina
Talla

A jawabin da ya gabatar gaban Majalisar Rasha da kusoshin gwamnatin kasar, Vladimir Putin ya bayyana cewa  kasashen yammacin na daukar dukkanin matakan da suke ganin za su taimaka musu wajen rusa Moscow, inda ya ce kai tsaye Rasha na da masaniya kan sashen da za ta farmaka a dukkanin kasashen don murkushe su.

Shugaba Putin ya bayyana cewa kasashen na yammacin har zuwa yanzu basu fahimci illar da katsalandan dinsu a yakin na Ukraine da Rasha ke haifar musu ba, hatta ga manufofinsu na cikin gida.

A cewar Putin yakamata kasashen yamma su sani cewa itama Rasha na da makamai kuma ta na da karfin soji haka zalika na nukiliya wadanda za ta iya amfani da su wajen farmakarsu kamar yadda suke tunanin za su iya yi wa Moscow rubdugu.

Tun farko kungiyar tsaro ta NATO ta gabatar da wani kudirin girke dakaru a Ukraine don taya kasar yakin da ta ke da Rasha sai dai tuni kasashen Amurka da Jamus da kuma Birtaniya suka ki amincewa da shi.

Kalaman na Putin da ke zuwa gabanin babban zaben Rasha na ranakun 15 zuwa 17 ga watan Maris, zaben da shugaban ke da tabbacin sake samun sabon wa’adin mulki na shekaru 6 ya nanata cewa Moscow ke da makamin nukiliya mafi karfi a duniya don haka babu wata fargaba a gareta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.