Isa ga babban shafi

An samu katsewar shafin Facebook a sassan duniya

Rahotanni na cewa an samu katsewar Facebook  ga dubban masu amfani da da shi, inda wasu a shafukan sada zumunta suka fara korafi saboda ba sa iya shiga shafukansu su a dandalin Meta.

Wata mace dauke da wayar salula da ke nuna tambarin Facebook a gaban kamfanin Meta.
Wata mace dauke da wayar salula da ke nuna tambarin Facebook a gaban kamfanin Meta. REUTERS - DADO RUVIC
Talla

Da dama daga cikin masu amfani da X sun bayyana irin rudanin da suka shiga, yayin da shafinsu na Facebook ya cire su daga shafin kai tsaye, kuma kokarin shiga ya ci tura.

Bugu da kari, masu amfani da shafin Instagram sun yi korafin cewa sun kasa komawa shafin farko ko kuma duba sabon abin da aka wallafa.

Wannan matsala ta kuma taba shafin Threads, wanda ke kamanceceniya da Twitter ko kuma X da aka kaddamar a shekarar bara.

Akwai tambayoyi da hasashe kan faruwar wannan al’amari da ala tilas ya haifar da katsewar shiga shafin na Facebook, inda a halin yanzu ake sa ran sanarwa daga kamfanin na Meta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.