Isa ga babban shafi

'Yan daba sun yiwa filin jirgin saman Haiti dirar mikiya

Kwana guda bayan da gungun ‘yan daba suka balle manyan gidajen yari biyu a Haiti, a yau kuma sun farwa babban filin jirgin saman kasar da nufin karbe iko da shi.

Yadda wasu fusatattun mutane suka gudanar da zanga-zanga a filin jirgin saman Antoine Simon Des Cayes da ke Les Cayes, na kasar Haiti, ranar 29 ga Maris, 2022
Yadda wasu fusatattun mutane suka gudanar da zanga-zanga a filin jirgin saman Antoine Simon Des Cayes da ke Les Cayes, na kasar Haiti, ranar 29 ga Maris, 2022 © John Cadafy Noel/AP
Talla

Wannan ta sa dole kasashen da ke makwaftaka da Haiti suka fara karfafa tsaron kan iyakokin su don gudun fantsamar ‘yan dabar zuwa cikin su.

Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda aka rika musayar wuta tsakanin jami’an sojoji da kuma ‘yan dabar sama da 500.

Har kawo yanzu filin jirgin saman na The Toussaint Louverture na kulle yayin da aka dakatar da duk wata zirga-zirga.

Ko a makon da ya gabata sai da ‘yan bindigar suka yi arangama da jami’an tsaro a filin jirgin, sai dai amarin bai yi muni irin na yau ba, abinda ke kara jefa fargaba game da yiwuwar ‘yan dabar su kwace iko da filin jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.