Isa ga babban shafi

Yau ake bikin ranar mata ta duniya

Ranar 8 ga watan Maris din kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don bikin ranar mata da ke da aniyar lalubo matsalolin da mata ke fuskanta da kuma duba hanyoyin warware su.Bikin ranar na bana dai ya zo ne a dai-dai lokacin da mata ke fuskantar matsin rayuwa sanadin tashe-tashen hankula da kuma tsananin talauci.

Yadda wasu mata a Lebanon suka gudanar da zanga-zangar neman tsagaita wuta a yakin Gaza.8/03/24
Yadda wasu mata a Lebanon suka gudanar da zanga-zangar neman tsagaita wuta a yakin Gaza.8/03/24 AP - Hussein Malla
Talla

A shekarar 1977 ne Majalisar Dinkin Duniya ta ga dacewar ware wannan rana da nufin girmama mata da kuma duba kan matsalolin da suke fuskanta tare da yunkurin shawo kansu.

Karfafawa mata gwiwa

Taken bikin na bana dai shi ne karfafawa mata gwiwa domin gaggauta samar da ci gaba a duniya, wanda yayi dai-dai da matsalolin rashin ilimi, cin zarafi, dunkufarwa da kuma zabtarwa da mata kan fuskanta a duniya yanzu haka.

Bikin na bana dai ya zo wa mata ne a dai-dai lokacin da rayuwar su ke kara tagayyara sanadin yake-yake, tsananin talauci da kuma fargaba ko kuma rashin tabbas na rayuwa cikin aminci da kuma yakinin tsare mutuntakar su.

Kasashen da mata suka fi fuskantar barazana

Majalisar Dinkin Duniya ta sanya kasashen Afghanistan, Pakistan da kuma Iran a matsayin kasashen da matan su suka fi fukantar barazanar rayuwa, yayin da suke fama da karancin kare hakkokin su.

A nahiyar Afrika kuwa matan kasashen Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Chadi da kuma Mali, sune suka fi rayuwa cikin tasku, tashin hankali da kuma tozarci a wasu lokuta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce lokaci ya yi da ya kamata a samarwa mata yanayin samun ilimi mai inganci, basu damar taka rawa wajen ci gaban al’umma, tsare mutuntakar su da kuma basu dama makamanciyar wadda ake baiwa twakarorin su maza.

Zanga-zanga

A wasu kasashe irinsu Lebanon mata sun gudanar da zanga-zanga neman kawo karshen kisan Falasdinawa a yankin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.