Isa ga babban shafi
YAKIN-GAZA

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani a kan harin Iran

Duniya – Majalisar dinkin duniya ta kira taron gaggawa domin nazari a kan hare haren da Iran ta kaiwa Isra'ila a matsayin ramako, yayin da kasashen duniya ke bayyana damuwa dangane da barazanar barkewar yaki a tsakanin kasashen biyu.

Yadda Isra'ila tayi ta kakkabo makamai masu linzamin da Iran ta harba mata
Yadda Isra'ila tayi ta kakkabo makamai masu linzamin da Iran ta harba mata REUTERS - Amir Cohen
Talla

Sakatare Janar na majalisar Antonio Guterres wanda ya yi Allah wadai da harin, ya bayyana damuwa dangane da barazanar tabarbarewar al'amura a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya bukaci bangarorin dake rikicin da su kai zuciya nesa.

Shugabar gudanarwar kungiyar kasashen Turai, Ursula von der Leyen ta bukaci Iran da ta gaggauta tsagaita wuta da kuma kiran bangarorin dake rikicin da su tsagaita wuta tare da aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Sakatare Janar na kungiyar kawancen tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg yace sun yi Allah wadai da abinda ya kira matakin na Iran, yayin da suke ci gaba da sanya ido a kan abinda ke faruwa a yankin.

Shugaban Amurka Joe Biden lokacin da yake jagorancn taron majalisar tsaron kasar
Shugaban Amurka Joe Biden lokacin da yake jagorancn taron majalisar tsaron kasar AP - Adam Schultz

Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya bayyana harin na Iran a matsayin na rashin hankali, wanda ke iya fadada tashin hankalin dake gudana a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da yace za suyi aiki tare da kawayen su domin kwantar da hankali.

Firaministan Canada Justin Trudeau ya soki harin na Iran, inda ya sake jaddada goyan bayan kasar sa ga Isra'ila.

Ita kuwa China ta bayyana harin na Iran a matsayin fadadar rikicin Gaza, inda ta bukaci aiwatar da kudirin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya domin tabbatar da tsagaita wuta da kuma kawo karshen tashin hankalin dake gudana a Gazar.

China ta bukaci kasashen duniya musamman masu karfin fada aji domin ganin sun taka rawar ganin wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin baki daya.

'Yan kasar Iran ke zanga zangar kyamar Isra'ila a gaban ofishin jakadancin Birtaniya dake Tehran
'Yan kasar Iran ke zanga zangar kyamar Isra'ila a gaban ofishin jakadancin Birtaniya dake Tehran via REUTERS - Majid Asgaripour

Kasar Masar ta bayyana matukar damuwa da tashin hankalin tare da gabatar da bukatar taka tsan tsan domin kaucewa jefa daukacin yankin cikin yaki.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da harin Iran a kan Isra'ila, wanda ya bayyana shi a matsayin abinda ka iya jefa daukacin yankin cikin tashin hankali.

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ya bayyana harin na Iran a matsayin rashin hankali da kuma kara da cewar babu dalilin daukar matakin.

Kasar Indonesia ta bi sahun sauran kasashen duniyar wajen bayyana matukar damuwa da harin da kuma bukatar kwamitin sulhu da ya gaggauta daukar mataki domin kwantar da rikicin dake gudana.

Shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei
Shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei © Khamenei.ir / AFP

Ita ma Rasha ta bayyana damuwa da harin, tare da samun taka tsan tsan, kamar yadda Qatar ta bukaci manyan kasashen duniya daukar matakin kwantar da hankalin bangarorin.

Kasar Saudi Arabia ta yi kira ga bangarorin biyu da su kai zuciya nesa domin kare yankin Gabas ta Tsakiya da mutanen sa daga barazanar yaki.

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cikakken goyan bayan sa ga Isra'ila bayan ganawa da manyan jami'an tsaron kasar, yayin da yace za su ci gaba da tallafawa kasar.

Sauran kasashen da suka bayyana matsayi dangane da harin sun hada da Ukraine da Turkiya da Spain da Italia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.