Isa ga babban shafi

Faransa na duba yuwuwar sauya wurin bikin bude gasar Olympics

A karon farko shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce za a iya sauya kogin Seine, da aka tsara gudanar da bikin bude gasar Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci, zuwa filin wasa na Stade de France saboda barazanar tsaro.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron daga tsakiya gabanin karbar bakuncin gasar Olympics ta 2024 da za a yi a birnin Paris.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron daga tsakiya gabanin karbar bakuncin gasar Olympics ta 2024 da za a yi a birnin Paris. © Yoan Valat/Pool via Reuters
Talla

Kwamitin shirya gasar ta Olympics da birnin Paris zai karbi bakunci dai ya shiya gudanar da gagarumin bikin bude gasar a kogin Seine, da a tarihi ba a taba yin irinsa a wajen filin da za a gudanar da wasannin gasar.

To sai dai gasar tazo ne a dai-dai lokacin da ake fuskantar riki tsakanin Rasha da Ukraine da kuma Isra’ila da Hamas a Gaza, lamarin da ya sanya hukumomin Faransa suka ce bikin bude gasar na cike da fuskantar barazanar hari.

A zantawar da aka yi da shugaba Macron a ranar Litinin din nan, ya ce suna da mabanbantan tsare-tsare da za su iya maye gurbin gudanar da budin bude gasar a kogin Seine.

Gasar ta Olympic za ta fara daga ranar 26 ga watan Yuli zuwa 11 ga Agustan 2024 a birnin Paris.
Gasar ta Olympic za ta fara daga ranar 26 ga watan Yuli zuwa 11 ga Agustan 2024 a birnin Paris. AP - Michel Euler

Akwai dai kimanin mutane dubu dari 3 da aka tsara su kasance a wajen bikin bude gasar, da kuma karin wasu dubu dari 2 da za su kalli bikin bude gasar daga gine-ginen da ke kusa da kogin Seine.

Kawo yanzu dukkanin kasashen da za su halarci gasar sun amince da kasance wa a bikin bude gasar da za a yi a Seine, cikinsu kuwa har da Amurka da Isra’ila da sukafi fuskantar barazana.

Sai dai shugaba Macron ya ce za su yi dukkanin abinda ya kamata, don ganin an samu tsaro da zaman lafiya a yayin gasar kamar yadda aka saba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.